Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Manyan batutuwan da Nijar ta sanya a ajandar shugabacin da zata jagoranta a watan na Disamba, sun hada da yaki da ta’addanci, sauyin yanayi.
A don haka ne kasar za ta shirya wani taron muhawara a ranar 9 ga wata kan tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, kamar yadda wakilin dindindin na kasar Malam Abdu Abari ya sanar yayin taron manema larabai.
Shugaban kasar Bazoum Mohamed ne zai jagoranci taron, tare da halartar babban sakataren MDD, da kuma shugaban kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika, inda ake sa ran kasashen duniya zasu tattauna hanyoyin kawo karshen ayyukan ta’addanci da kuma shinfida zaman lafiya mai daurewa a duniya, da kuma vatun canjin yanayi.
A dayen bangaren kuma Nijar ta yi fatan tattaunawar neman farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka fara a Vienna ta haifar da da mai ido.
342/